Abba Kyari ya bayyana abinda ya ke ci ma sa tuwo a aikin dan sanda

Abba Kyari ya bayyana abinda ya ke ci ma sa tuwo a aikin dan sanda

A jiya, Asabar, ne babban jami’in dan sanda Abba Kyari ya wallafa wani rubutu a shafinsa na facebook da ke bayyana takaicin sa a kan yadda manyan ‘yan ta’adda ke canja jawabin amsa laifinsu duk lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu.

A mtsayina na lauya abun ya kan bani dariya duk lokacin da naga ‘yan fashin daka kama na garin Offa na kokarin canja jawabin su a gaban kotu. Wannan shine abinda yake faruwa koda yaushe a kotunan mu. Hakan ta faru a kan kasurgumin mai garkuwa da mutanen nan da ake kira Evans lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu.

“Ya kamata dukkan ‘yan Najeriya su sani cewar a duk lokacin da aka gurfanar da babban dan ta’adda a gaban kotu ba ya amsa laifin sa; ‘yan fashi basa amsa laifinsu a kuma basa taba fadin alheri a kan dan sanda ko duk mutumin da ya kama su.

Abba Kyari ya bayyana abinda ya ke ci ma sa tuwo a aikin dan sanda
'Yan fashin garin Offa
Asali: Depositphotos

“Idan ka ji dan fashi ko mai garkuwa da mutane ya fadi alheri a kan dan sanda to kyale shi ya yi bai kama shi ba ko kuma yana bashi hadin kai wajen aikata ta’addancin da yak e yi ko kuma cin hanci ya karba ya sake shi bayan ya kama shi.

Yanzu ya zama ruwan dare ga kowanne dan ta’adda ya musanta jawabin da ya bayar ga ‘yan sanda bayan an gurfanar da shi a gaban kotu duk da irin tarin dumbin shaidar da ake da ita a kan sa kamar yadda za mu iya gani a kan Evans da ‘yan fashin Offa da na’uarar daukan faifan bidiyo ta nade su yayin da suke aikata fashi da makami a bankuna.

DUBA WANNAN: Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga APC

“A duk jawaban rundunar ‘yan sanda a kan fashin garin Offa, babu inda ta ambaci cewar Saraki ne ya basu bindigun da suka yi fashi amma su ‘yan fashin ne da kan su suka bayyana hakan a jawabinsu da kuma a lokacin da manema labarai ke ganawa da su. Sun shaida wa duniya cewar su ‘yan dabar siyasa ne na Saraki kuma shine ke basu kudi, sun halarci bikin diyar sa kuma da su aka raka shi yiwa sarkin Offa jajen fashin, hatta motar da su ka je fashin da ita sun bayyana cewar Saraki ne ya basu."

Abba Kyari ya ce ya bayyana haka ne domin wayar da kan jama’a a kan abinda kafafen yada labarai ke wallafa wa a shafukan jaridun su dangane da fashin garin Offa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel