Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC

Jam'iyyar APC mai mulki ta zargi Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Muhammad Wakili da hannu dumu-dumu wurin taimakawa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP tafka mugudin zabe a zaben gwamna na jihar Kano.

Sakataren jam'iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi inda ya ce kwamishinan 'yan sandan ya janye masu tsaron kwamishinan jihar Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC
Da duminsa: CP Singham Wakili ya taimaki PDP tayi mana magudi a Kano - APC
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan takarar gwamna 20 sun goyi bayan maimaita zabe a Bauchi

"Ba boyeyen abu bane yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Kano yana da hannu wurin taimakawa jam'iyyar PDP yin magudin zabe a cikin birnin Kano ta hanyar baiwa magoya bayan Kwankwaso kariya yayin da ya janye masu tsaron kwamishinan jihar Kano," inji shi.

"Nasororin da da jam'iyyar APC ta samu karkashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje sun isa su bashi nasarar a zaben da za a maimaita.

"Kuma za a maimaita zaben ne a kauyukan da jam'iyyar APC ta ke da magoya baya sosai da karamar hukumar Nasarawa inda mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya fito. Babu shakka, jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da APC ke da karfi kuma har yanzu mu ke da jihar," inji Issa-Onilu.

Ana dai ganin Wakili shine jarumin babban zaben 2019 saboda 'yan sanda karkashin jagorancinsa sun kama mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Gawuna da Kwamishinan Kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Lamin Sani da aka ce wai ya yaga sakamakon zabe a lokacin da ake kidiya kuri'un na karamar hukumar Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel