Sanin makamar aiki: Yawan litar man da aka samar wa 'yan Najeriya a watan Disemba

Sanin makamar aiki: Yawan litar man da aka samar wa 'yan Najeriya a watan Disemba

Akalla litar man fetur biliyan da da miliyan dari takwas (Biliyan 1.8) ne hukumar rukunin kamfanonin albarkatun man fetur na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) suka ce sun shigo da su a watan Disembar da ta gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin mujallar da hukumar rukunin kamfanonin kan fitar ta wata-wata na watan Disemba din dauke da sauran bayanai da suka hada da yawan man fetur din da aka sha a kasar da kuma yawan kudaden da kasar ta samu sanadiyyar hakan.

Sanin makamar aiki: Yawan litar man da aka samar wa 'yan Najeriya a watan Disemba
Sanin makamar aiki: Yawan litar man da aka samar wa 'yan Najeriya a watan Disemba
Asali: UGC

KU KARANTA: An samu gobara a garin Bogocho

Haka zalika da jami'in hulda da jama'a na NNPC din, Mista Ndu Ughamadu yake karin fashin baki akan rahoton dake cikin mujallar, ya bayyana cewa kullum miliyan 58 yan Najeriyar suka rika sha a watan na Disemba.

Ya kara da cewa hukumar ta kara yawan man da ke shigowa da shi ne a watan na Disemba wanda hakan mai rasa nasaba da matsalar man fetur da akan yi a duk shekara amma shekarar da ta gabata ba'ayi hakan ba.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta karyata labarin dake yawo a kafafen yada labarai na cewa jami'an ta sun kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel