Zaben 2019: ‘Ya ‘yan PDP su na so a canza Shugaban jam’iyya a Edo

Zaben 2019: ‘Ya ‘yan PDP su na so a canza Shugaban jam’iyya a Edo

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata kungiyar ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Edo da ke cikin Kudancin Najeriya ta na so shugaban babban jam’iyyar adawa ta jihar yayi maza ya rubuta takardar murabus.

Zaben 2019: ‘Ya ‘yan PDP su na so a canza Shugaban jam’iyya a Edo
Nasarar APC ta sa an taso Shugaban PDP a gaba ya sauka a Edo
Asali: UGC

Wannan kungiya ta Edo PDP Parliament for Positive Change, tayi kira ga shugaban PDP na jihar Edo gaba daya watau Cif Dan Orbih da ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyya saboda faduwa zabe da PDP tayi a zaben bana.

KU KARANTA: Babban Kotun daukaka kara ta ba 'Dan takarar PDP gaskiya

Kungiyar da ke kokarin ceto jam’iyyar a jihar Edo ta koka da halin da aka jefa PDP na rashin lashe zabe. Barr. Davison Osas, wanda yana cikin manyan jagororin wannan kungiya yace burin su shi ne kokarin farfado da jam’iyyar.

A wani jawabi da Davison Osas ya fitar, yace Dan Orbih yayi shekaru 9 a matsayin shugaban PDP a Edo amma babu abin kirkin da ya iya yi wa jam’iyyar, ganin yadda aka kifar da jam’iyyar da kasa a zaben ‘yan majalisar dokoki.

Har dai ta kai wannan kungiya tana zargin Cif Orbih da hada-kai da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole wajen rashin da PDP take samu. Osas yace dole D. Orbih ya sauka musamman ganin yadda ya dade a kan kujerar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel