Malaman darikan kotolika sun aike da sako game da zabe ga Buhari

Malaman darikan kotolika sun aike da sako game da zabe ga Buhari

Malaman darikar Katolika na Najeriya sun shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kuma ya amince da sabbin dokokin zabe domin tabbatar da cewa an samu sahihiyar zabe mai tsafta a nan gaba.

Malaman addinin sun ce daya daga cikin babban matsalar da aka samu yayin zaben ita ce matsalar sayan kuri'u da wasu 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa masu haddama ke yi domin ganin sun samu mulki ta ko wane hali.

Sun bukaci gwamnati ta amince da matsalolin da aka samu a zaben 2019 sannan ta dauki hanyar magance su saboda gaba.

Malaman darikan kotolika sun aike da sako game da zabe ga Buhari
Malaman darikan kotolika sun aike da sako game da zabe ga Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Kamar yadda ya ke cikin sakon bayan taron da kungiyar malaman darikan na katolika, CBCN suka gudanar a Abuja mai dauke da sa hannun shugaban CBCN, Most Rev. Augustine Akubeze da sakataren kungiyar, Rev. Camilus Umoh:

"Mun amince cewa zabe dama ce da ake baiwa al'umma su zabi wadanda suke so su jagorance su.

"Mun lura akwai kallubale da yawa da suka taso yayin zaben wadanda suka taso saboda rashin dokokin zabe da hakan ya baiwa wasu masu mugun nufi damar tafka magudi domin suyi nasara.

"Ko a lokutan da akwai doka, galibi ba a biyaya ga dokan. Wani mummunan abu da aka rika samu yayin zabe shine saya da sayarwan kuri'u da wasu yan siyasa da jam'iyyu masu hadama suka rika yi domin su samu mulki a kowanne hali.

"Zabe marasa inganci ba su haifar da shugabanni na gari. Muna kira da gwamnati ta amince da matsalolin da aka samu yayin zaben 2019 sannan ta dauki hanyar gyara su.

"Muna kira da gwamnati ta zartar da dokoki zaben da za su tabbatar an gudanar da zabe mai tsafta da inganci a nan gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel