Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga APC

Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada wa mambobin jam’iyyar sa, APC, cewar ba zai saka baki a zabukan da za a maimaita a wasu jihohin kasar nan ba.

A wani jawabi da kakakin sa, Malam Garba Shehu, ya fitar a yau, Lahadi, Buhari ya bayyana cewar ba zai yi Magana da hukumar zabe ta kasa (INEC) ba domin ta yi alfarma ga ‘yan takarar jam’iyyar APC ba.

A cikin jawabin, shugaba Buhari ya gargadi ‘yan siyasa a jihohin da za a maimaita zabukan da su guji amfani da kalaman da kan iya tunzura ma su zabe gabanin zabukan da za a maimiata.

Kazalika, jawabin ya yi tir da kalaman wadan su, musamman ‘ya’yan jam’iyyar APC, da ke sukar shugaba Buhari a kan ya ki saka baki domin ‘yan takarar jjam’iyyar APC su sami alfarma.

Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga EFCC
Buhari
Asali: Twitter

Shehu ya kara da cewa: “tsofin shugabannin Najeriya na baya na saka baki a duk lokacin da za a maimaita zabe, kuma hakan ne ya sa wasu ke ganin laifin shugaba Buhari yanzu saboda bai saka baki b aba tare da sun yi la’akari da cewar shugaba Buhari daban yake ba. Ya yi rantsuwa a kan kare martabar kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ba zai yi duk wani abu da ya saba wa haka ba.

Kundin tsarin mulkin Najeriya bai bawa shugaban kasa ikon yin haka ba. Abun dariya ne da ban mamaki a soki shugaba Buhari a kan bai yiwa kundin tsarin mulki karan tsaye ba.

DUBA WANNAN: Zan shiga APC tare da duk magoya baya na - Jagoran kamfen din Atiku na kasa

“Wani abun mamaki ma shine yadda ‘yan jam’iyyar adawa ke suka da zargin shugaba Buhari a kan yana son yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin bawa ‘yan takarar jam’iyyar APC sukunin lashe zabe.”

“Ya kamata ‘yan APC a jihohin da za a maimaita zabe su sani cewar alhakin jam’iyya ne ta yi aiki tukuru domin tabbatar da samun nasara ba wai zaman jiran tsammanin shugaba Buhari ya umarci INEC ta murde zabe ko yin alfarma ga ‘yan takarar APC ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel