Hukumar EFCC ta karyata kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen

Hukumar EFCC ta karyata kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta karyata labarin dake yawo a kafafen yada labarai na cewa jami'an ta sun kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen.

Jami'in hukumar ta EFCC dake magana da yawun ta, Mista Tony Orilade shine ya bayyana hakan ga wakilin majiyar mu ta Channels ta wayar tarho inda yace labarin bai da tushe balle makama kuma ya bukaci al'ummar kasa da su yi watsi da shi.

Hukumar EFCC ta karyata kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen
Hukumar EFCC ta karyata kai samame gonar tsohon alkalin alkalai Onnoghen
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben Ribas: APC ta karyata INEC

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun kawo maku labarin cewa Jami’an hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya, sun kai samame kan gonar Alkalin Alkalan kasar da aka dakatar, Walter Onnoghen dake jihar Nasarawa.

A labarin wanda aka buga da ranar yau, munce jami'an na EFCC sun gudanar da bincike tare da tafiya da wasu takardu da suka shafi hada hadar kudade.

Cikin watan Janairu da ya gabata, Gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da Walter Onnoghen daga matsayinsa na alkalin alkalai, har sai yak are kansa daga zargin cin hanci da rashawa, da ki bayyana wasu kadarori da ya mallaka, a gaban kotun da’ar ma’aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel