Chidi Lloyd ya roki afuwar Buhari, ya gargadi Magnus Abe da ya fita sha'aninsa

Chidi Lloyd ya roki afuwar Buhari, ya gargadi Magnus Abe da ya fita sha'aninsa

- Chidi Lloyd, babban daraktan yakin zaben Tonye Cole, ya roki shugaban kasa Buhari, da ya gafarta masa akan irin sukarsa da ya rinka yi masa

- Llyod ya kuma zargi Magnus Abe, da hada baki da Nyesom Wike domin karya lagon nasarar APC a jihar

- Lloyd ya yi nuni da cewa shi balagaggen mutum ne, wanda kuma ya ke da ikon yin tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a cikin kasar

Chidi Lloyd, babban daraktan yakin zaben Tonye Cole, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya gafarta masa akan irin sukarsa da ya rinka yi na tsawon lokaci da kuma nuna masa kiyayya mai tsanani.

Llyod ya kuma zargi Magnus Abe, dan takarar gwamnan jihar Rivers karkashin jam'iyyar APC, da hada baki da Nyesom Wike, dan takarar gwamnan jihar karkashin PDP, domin karya lagon nasarar APC a jihar yana mai kira ga Abe da hawainiyarsa ta kiyayi ramarsa.

Ya kuma caccaki Abe da wani yunkuri na sauya kalamansa da ra'ayinsa ya zuwa iri daya da na Rotimi Ameachi, ministan Nigeria kan harkokin zirga zirga kuma daya daga cikin jagororin APC a jihar.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: INEC ta sanar da ranar sake zaben majalisun dokoki na jihar Ekiti

Chidi Lloyd ya roki afuwar Buhari, ya gargadi Magnus Abe da ya fita sha'aninsa
Chidi Lloyd ya roki afuwar Buhari, ya gargadi Magnus Abe da ya fita sha'aninsa
Asali: Depositphotos

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema abarai a wannan makon, Lloyd ya yi nuni da cewa shi balagaggen mutum ne, wanda kuma ya ke da ikon yin tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a cikin kasar.

Ya ce: "Kowa ya na sane da cewa muna aiki tukuru domin ganin cewa shugaban kasa Buhari ya zarce, amma shi Magnus Abe ya gana da tawagar kodinetoci guda 23 daga kanana hukumomi 23 a sansaninsa da su je kananan hukumominsu tare da umurtar magoya bayansu da su zabi Atiku maimakon shugaban kasa Buhari, kuma hakan suka yi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel