Da zafinsa: INEC ta sanar da ranar sake zaben majalisun dokoki na jihar Ekiti

Da zafinsa: INEC ta sanar da ranar sake zaben majalisun dokoki na jihar Ekiti

- INEC ta ce ta sanya ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da zata gudanar da zaben kujerun majalisun dokoki na jihar Ekiti

- Hukumar ta kuma baiwa jam'iyyun siyasa tabbacin cewa za ta yiwa kowacce jam'iyya adalci a yayin gudanar da zaben zagaye na biyu

- Ta ce zaben zai gudana ne a rumfunan zabe guda biyar da ke a cikin mazabar, kamar yadda shugaban hukumar Mahmood Yakubu ya bayar da umurni

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a ranar Lahadi ta ce ta sanya ranar 23 ga watan Maris a matsarin ranar da zata gudanar da zaben kujerun majalisun dokoki na jihar Ekiti kadai, da ba a kammala gudanarwa a ranar 9 ga watan Maris ba.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben mazabar Ekiti ta Gabas ta 1 a matsayin zaben da bai kammala ba sakamakon rahoton rikici da kuma wasu dalilai.

Sakataren mulki na INEC da ke jihar, Muslim Omoleke, wanda kuma shine mukaddashin kwamishinan hukumar a jihar ya sanar da sabuwar ranar sake zaben a garin Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

KARANTA WANNAN: Sake zaben Kano: Ganduje ya kaddamar da manyan ayyuka a mazabun da aka soke zabensu

Fafesa Mahmood Yakubu: Shugaban hukumar INEC
Fafesa Mahmood Yakubu: Shugaban hukumar INEC
Asali: Twitter

Ya bukaci 'yan siyasa da za su shiga cikin zaben da za a sake gudanarwar da su daura damarar tarbar wannan rana.

Ya kuma baiwa jam'iyyun siyasa tabbacin cewa hukumar ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen yiwa kowacce jam'iyya adalci a yayin gudanar da zaben zagaye na biyu.

Mr Omoleke ya ce zaben zai gudana ne a rumfunan zabe guda biyar da ke a cikin mazabar, kamar yadda shugaban hukumar INEC na kasa Mahmood Yakubu ya bayar da umurni.

Mukaddashin kwamishin hukumar na jihar ya ce INEC za ta gana da jami'an tsaro a cikin makon nan tare da yi masu bayani kan bukatar zage damtsensu domin fuskantar zaben kujerun majalisun dokokin jihar da za a sake gudanarwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel