Zan shiga APC tare da duk magoya baya na - Jagoran kamfen din Atiku na kasa

Zan shiga APC tare da duk magoya baya na - Jagoran kamfen din Atiku na kasa

Kasa da sa’o’i 24 bayan ya bayyana cewar ya bar jam’iyyar PDP tare da yin murabus daga harkokin siyasa, tsohonn gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel, ya amince ya jagoranci magoya bayansa zuwa jam’iyyar APC.

Legit.ng ta rawaito cewar Gbenga Daniel, darekta janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya sanar da yanke shawarar yin murabus daga zama mamba a jam’iyyar APC da harkokin siyasa.

Jim kadan bayan Daniel ya fitar da wannan sanarwa, gwamnan jihar Ogun da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar APC, Dapo Abiodun, ya kai ma sa wata ziyara a jiya, Asabar, a gidan sa dake Legas in da suka yi wata ganawar sirri.

Zan shiga APC tare da duk magoya baya na - Jagoran kamfen din Atiku na kasa
Dapo Abiodun da Gbenga Daniel
Asali: Twitter

A takardar da ya aike ga uwar jam’iyya ta kasa a ranar 14 ga watan Maris, Daniel ya bayyana cewar ya yanke shawarar barin jam’iyyar PDP ne bisa radin kan sa domin ya mayar da hankali a kan wasu harkokin rayuwa.

Kazalika ya bayyana cewar zai yi amfani da lokacin da zai samu domin farfado da kungiyar sa ta jin kai, ‘Gateway Fron Foundation (GFF)’ tare da bayyana cewar zai dawo da aiyukan wata cibiya mai suna ‘non partisan Political Leadership Academy (POLA)’ da aka kafa a wasu shekarun baya domin ilimantar da ‘yan kasa a kan harkokin siyasa.

DUBA WANNAN: ‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32

Sai dai, a yau, Lahadi, sai gas hi Daniel ya yi mi’ara koma baya tare da bayyana cewar zai jagoranci magoya bayansa zuwa jam’iyyar APC.

Daniel ya canja shawara ne bayan dumbin magoya bayan sa sun bayyana cewar basu yarda da shawarar cewar zai bar siyasa ba.

Da yake ganawa da dumbin magoya bayansa a yau, Lahadi, Daniel ya ce yana yin siyasa ne don jama’a kuma zai yi duk abinda suke so.

Dumbin magoya bayan Daniel ne suka hau ihun nuna rashin goyon bayansa yayin da yake sanar da su shawarar sa na yin murabus daga siyasa, lamarin da ya kai tilas ya bar wurin taron ba tare da ya kamala jawabi ba.

Da manema labarai suka tambaye shi ko wacce shawara zai yanke a kan bukatar da magoya bayansa suka bijiro da ita, sai ya kada baki ya ce; “zan yi duk abinda mutane na ke so.”

“To me zan ce? Jama’a ta sun riga sun yanke hukunci,” yayin da yake amsa tambayar manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel