Sake zaben Kano: Ganduje ya kaddamar da manyan ayyuka a mazabun da aka soke zabensu

Sake zaben Kano: Ganduje ya kaddamar da manyan ayyuka a mazabun da aka soke zabensu

- Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da manyan ayyuka a gundumar Gama a yayin da ake shirye shiryen kaddamar da zaben jihar Kano zagaye na biyu

- Akalla manyan ayyuka guda ukku da suka hada da kwashe shara, gina fanfunan tuka-tuka da kuma sake ginin hanyoyi, gwamnatin ta kaddamar a gudnumar

- An soke zaben gundumar Gama bayan kammala zaben gwamnoni da ya gudana a ranar 9 ga watan Maris

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da manyan ayyuka a gundumar Gama da ke karamar hukumar Nassarawa, a yayin da ake shirye shiryen kaddamar da zaben jihar Kano zagaye na biyu, wacce ake kallon gundumar a matsayin babbar gundumar da zabenta ke da muhimmanci.

Akalla manyan ayyuka guda ukku da suka hada da kwashe shara, gina fanfunan tuka-tuka da kuma sake ginin hanyoyi, gwamnatin ta kaddamar da su a cikin kwamnaki ukku da suka gabata a cikin garin.

An soke zaben gundumar Gama bayan kammala zaben gwamnoni da ya gudana a ranar 9 ga watan Maris.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Wani dan bindiga ya kashe dan sanda a Bayelsa, ya sace bindigarsa

Sake zaben Kano: Ganduje ya kaddamar da manyan ayyuka a mazabun da aka soke zabensu
Sake zaben Kano: Ganduje ya kaddamar da manyan ayyuka a mazabun da aka soke zabensu
Asali: Twitter

Soke zaben ya biyo bayan wani hari da aka kai a cibiyar tattara sakamakon zaben karamar hukumar a ranar 11 ga watan Maris bisa jagorancin manyan jami'an gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Ana sa ran mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ne ya jagoranci kai harin, wanda ya kai ga har an yaga sakamakon zaben gundumar a cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Rundunar 'yan sanda ta cafke kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Garo da shugaban karamar hukumar, Lamin Sani a harabar cibiyar tattara sakamakon inda har rundunar ta fitar da sanarwa na tabbatar da sa hannun Garo da Sani tare da shan alwashin gurfanar da su gaban kotu da zaran ta kammala bincike.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel