Sake Zabe a jihohi 6: Ba haka muka so ba, amma nasara na tare da mu

Sake Zabe a jihohi 6: Ba haka muka so ba, amma nasara na tare da mu

Ba ya ga bayyana rashin jin dadin hukuncin da hukumar INEC ta yanke na sake zaben gwamna a wasu jihohi shida na kasar nan, jam'iyya mai ci ta APC ta tabbatar da yakinin samun nasara yayin sake gudanar da zaben a mako mai zuwa.

Jam'iyya mai ci ta APC ta bayyana rashin jin dadi gami da cewar hukumar INEC ta sha kunyar gaske biyo bayan hukuncin da ta yanke na maimata zaben gwamna cikin wasu jihohi 6 na kasar nan.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu Mahmood
Asali: Twitter

Kakakin jam'iyyar na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, shi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi yayin ganawar sa da manema labarai na kafar watsa labari ta Channels TV.

Cikin gabatar da jawaban sa na yakini tare da tabbacin samun nasarar jam'iyyar APC, Mista Lanre ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC da ta tabbatar da tsarkakken zabe na gaskiya yayin maimacin sa a jihohin Adamawa, Bauchi, Benuwe, Kano, Filato da kuma Sakkwato.

KARANTA KUMA: Buhari zai inganta gine-ginen manyan tituna da ke Kudu maso Gabas - Onochie

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, jam'iyyar APC na ci gaba da zargin jam'iyyar adawa ta PDP da kulla kitimurmurar tafka magudi da duk wani nau'i na rashin gaskiya domin rinjayar da nasarar sakamakon zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel