Ba ruwan sojoji a zaben da aka gudanar - Wani babban dan siyasa a kudu

Ba ruwan sojoji a zaben da aka gudanar - Wani babban dan siyasa a kudu

Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Rear Admiral John Jonah mai ritaya ya bukaci 'yan Najeriya da su dena ganin laifin sojoji musamman ma wajen gudanar da zabukan da suka gabata na 2019.

Mataimakin gwamnan na jihar dai ya bayya hakan ne a ranar Asabar din da ta gabata a garin Yanogoa, babban birnin jihar Katsina lokacin da yake kaddamar da wasu ayyukan cigaba a barikin sojojin dake jihar na 16 da ake cewa “Tukur Buratai Camp”.

Ba ruwan sojoji a zaben da aka gudanar - Wani babban dan siyasa a kudu
Ba ruwan sojoji a zaben da aka gudanar - Wani babban dan siyasa a kudu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Na hannun damar Buhari ya ce Gwamnan Adamawa ya yadda ya fadi

Ya cigaba da cewa a kashin kansa yayi bincike kan zargin da aka yi na shigar sojojin harkokin zaben kuma ya ce bai ga inda sojojin suka yi laifi ba kamar dai yadda Hafsan sojojin kasar, Laftanal Janar Tukur Buratai ya ce.

Daga karshe kuma shi mataimakin gwamnan ya bukaci 'yan kasar da su cigaba da baiwa sojojin kasar dukkan goyon bayan da ya kamata domin samun zaman lafiya mai dorewa.

A wani labarin kuma, Jama'iyyar adawa a jihar Ribas ta All Progressives Congress (APC) ta karyata kalaman hukumar dake zaman kanta ta kasa dake da alhakin gudanar da zabe ta Independent National Electoral Commission (INEC) akan shigar sojoji cikin harkar zaben gwamnan jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban Daraktan jam'iyyar dake kula da harkokin yada labarai na dan takarar gwamnan jihar a APC, Mista Tonye Cole mai suna Tonye Prince will ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel