Da duminsa: Wani dan bindiga ya kashe dan sanda a Bayelsa, ya sace bindigarsa

Da duminsa: Wani dan bindiga ya kashe dan sanda a Bayelsa, ya sace bindigarsa

Awanni kan bayan da aka kai wani hari a wani Otel da ke garin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda biyu, rahotanni sun bayyana cewa an harfe wani d'an sanda da ke tsaron wani katafaren shagon sayar da kayayyaki (Joepal Supermarket) da ke a yankin Amarat, Yenagoa, a ranar Juma'a.

Bayan kashe d'an sandan, rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da bindigarsa.

Wannan sabon harin dai na zuwa ne jim kadan baya da aka kashe wasu 'yan sanda guda biyu da ke tsaron Udeme Hotels, mallakin Sanata Emmanuel Puller, inda aka kashe su tare da yin awon gaba da bindigoginsu.

KARANTA WANNAN: Jam'iyyar PDP ta zargi Okorocha da cire 17bn cikin kwanaki 2 daga lalitar jihar

Da duminsa: Wani dan bindiga ya kashe dan sanda a Bayelsa, ya sace bindigarsa
Da duminsa: Wani dan bindiga ya kashe dan sanda a Bayelsa, ya sace bindigarsa
Asali: Depositphotos

Haka zalika, kafin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabreru, an kai wa wata girkar binciken 'yan sanda da ke karkashin gadar Julius Berger da ke a cikin jihar hari, wanda ya yi sanadin mutuwar dan sanda daya tare da jikkata wani, inda aka sace bindigogi biyu yayin harin.

Majiya daga rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa akalla bindigogi biyar ke nan na 'yan sanda aka yi awon gaba da su a cikin makwanni ukku, sakamakon hare haren da ake kaiwa jami'an rundunar.

Wani babban jami'i a rundunar 'yan sanda ta jihar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa wata kungiyar asiri ce da ke a jihar mai daukar wadanne hare hare da kuma sace bindigogin tare da kashe jami'an rundunar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel