Na hannun damar Buhari ya shawarci Gwamnan Adamawa na APC ya yadda ya mika mulki da PDP

Na hannun damar Buhari ya shawarci Gwamnan Adamawa na APC ya yadda ya mika mulki da PDP

Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya kuma daya daga cikin na hannun damar shugaba Muhammadu Buhari, Mista Babachir Lawal ya shawarci gwamnan jihar Adamawa kuma dan jam'iyyar APC, Gwamna Muhammad Bindow ya mikawa PDP mulkin jihar kawai.

A cewar sa, yana shawartar gwamnan da ya yadda da sakamakon zaben da aka gudanar inda jam'iyyar sa ta APC din ta sha kaye a hannun jam'iyyar PDP domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Na hannun damar Buhari ya shawarci Gwamnan Adamawa na APC ya yadda ya mika mulki da PDP
Na hannun damar Buhari ya shawarci Gwamnan Adamawa na APC ya yadda ya mika mulki da PDP
Asali: Facebook

KU KARANTA: Duk na tare da Saraki ba zai mulki majalisa ba - Omo Agege

Mista Babachir din dai ya bayyana cewa a bisa alkalumman da suka bayyana yana da matukar wahala ace gwamnan ya lashe zaben da za'a sake yin zagaye na biyu musamman ma ganin duka duka wadanda suka yi rijista a rumfunan zaben 44 da za'a sake zaben duka duka 34,101 ne.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jami'in dake tattara sakamakon zabukan hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta Adamwa a satin da ya gabata ya bayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammalu ba.

A wani labarin kuma, Jama'iyyar adawa a jihar Ribas ta All Progressives Congress (APC) ta karyata kalaman hukumar dake zaman kanta ta kasa dake da alhakin gudanar da zabe ta Independent National Electoral Commission (INEC) akan shigar sojoji cikin harkar zaben gwamnan jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban Daraktan jam'iyyar dake kula da harkokin yada labarai na dan takarar gwamnan jihar a APC, Mista Tonye Cole mai suna Tonye Prince will ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel