Jam'iyyar PDP ta zargi Okorocha da cire 17bn cikin kwanaki 2 daga lalitar jihar

Jam'iyyar PDP ta zargi Okorocha da cire 17bn cikin kwanaki 2 daga lalitar jihar

- Jam'iyyar PDP a jihar Imo ta daga jijiyoyin wuya kan wani zargi da ta ke yi na cewar an cire sama da 17bn daga bankunan ajiya na jihar a cikin kwanaki biyu

- PDP ta kuma yi zargin cewa Okorocha tare da 'yan kazaginsa sun tura abeben hawa mallakin gwamnati wa wasu 'yan jihar bayan sunyiwa ababen hawar sabuwar rejista

- Da wannan, jam'iyyar ta gargadi bankuna da sauran hukumomin da ke harkallar kudade da su guji alaka da gwamnan wajen ci gaba da wawure dukiyar jihar

Jam'iyyar PDP a jihar Imo ta daga jijiyoyin wuya kan wani zargi da ta ke yi na cewar an cire sama da 17bn daga bankunan ajiya na jihar a cikin kwanaki biyu.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun babban lauya Charles Ezekwm, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Imo, "daga ranar 12 ga watan Maris da ranar Alhamis 14 ga watan Maris 2019, gwamna Rochas Okorocha ya cire kudade daga bankunan Access, Zenith, Unity da kuma bankin Skye wanda suka haura 17bn."

Sanarwar ta kara da zargin cewa a cikin kwanakin biyu, gwamnan tare da 'yan kazaginsa sun tura abeben hawa mallakin gwamnati wa wasu 'yan jihar bayan sunyiwa ababen hawar sabuwar rejista.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya

Jam'iyyar PDP ta zargi Okorocha da cire 17bn cikin kwanaki 2 daga lalitar jihar
Jam'iyyar PDP ta zargi Okorocha da cire 17bn cikin kwanaki 2 daga lalitar jihar
Asali: UGC

Ta kara da cewa kayayyakin gwamnati da suka hada da kayayyakin amfanin cikin gida da ofis da kuma kayan wuta da ke a cikin gidan gwamnatin jihar da ke Owerri, an kai su gidansa da ke Ogboko, karamar hukumar Ideota ta Kudu.

PDP reshen jihar Imo, ta kuma zargi Okorocha a cikin sanarwar da karkatara da dukkanin manyan na'urorin rarraba wutar lantarki da suka kai 300 da ke a cikin gidan gwamnatin jihar zuwa gidansa da ke Ideato ta Kudu.

A cewar sanarwar, gwamnan mai barin gado ya dage wajen daukar sabbin ma'aikata, inda takardun daukarsu aiki ta ke da kwanan watan baya da nufin haddasa fitina ga gwamnan jihar mai jiran gado.

Da wannan, jam'iyyar ta gargadi bankuna da sauran hukumomin da ke harkallar kudade da su guji alaka da gwamnan wajen ci gaba da wawure dukiyar jihar, tana mai cewa duk bankin da aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel