Kisan mutane 30 a Kaduna: Buhari ya bawa ma su kai hari shawara

Kisan mutane 30 a Kaduna: Buhari ya bawa ma su kai hari shawara

A jiya, Asabar, ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kasha mutane 10 a garin Nandu-Gbok dake karamar hukumar Sanga mai iya da jihohin Nasarawa da Filato a jihar Kaduna.

Dakta Hadiza Balarabe, sabuwar mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa’i, ‘yar asalin karamar hukumar Sanga ce.

An kona gidaje fiye da 30 a harin kamar yadda dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP da mai wakiltar yankin a majalisar wakilai ta suka tabbatar.

Samuel Aruwan, babban mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya tabbatar da kai harin a cikin wani jawabi da ya fitar domin mika sakon jajen gwamnati ga jama’ar yankin da harin ya shafa ko ya ritsa da ‘yan uwansu.

A nasa bangaren, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi Alla-wadai da kai harin tare bawa masu kai hare-hare a jihar Kaduna shawarar su dakata haka.

Kisan mutane 30 a Kaduna: Buhari ya bawa ma su kai hari shawara
Buhari
Asali: Twitter

Lamarin kai hare-hare da kisan rai da zubar da jinni na matukar damu na, na kasa fahimtar yadda wasu mutane ke kisa haka kurum ba tare da la’akari da girma ko muhimmanci ‘rai’ ba,” a cewar shugaba Buhari ta bakin babban mai taimaka ma sa bangaren sadarwa da yada labarai.

Sannan ya cigaba da cewa; “babu wani shugaba mai kishin jama’ar sa da zai kwanta cikin farinciki yayin ‘yan kasar sa ke kasha kan su saboda banbancin kabila ko kuma addini.”

DUBA WANNAN: Binciken daloli: EFCC ta kai same gida da gidan gonar tsohon alkalin alkalai

“Matukar babu wani bangare da zai iya hakuri a kan banbancin dake tsakaninsa da abokan zamansa, ba za a daina samun irin wadannan kai hare-hare ba.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnati na cigaba da neman hanyar da zata bi don kawo karshen wannan matsalar tare da yin kari da cewar, “wadanda matsalolin suka shafa basa bawa kokarin gwamnati hadin kai ta hanyar siyasantar da duk yunkuri da gwamnati ta yi domin kawo karshen matsalar.”

“An siyasantar da komai a Najeriya, hatta kokarin gwamnati na tabbatar da adalci a tsakanin jama’ar kasa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel