Gwamnonin da na neman yi wa Jam’iyyar APC taron dangi a Majalisa ta 9

Gwamnonin da na neman yi wa Jam’iyyar APC taron dangi a Majalisa ta 9

- Ana cigaba da lissafin wanda za su shugabanci majalisa ta 9 a Najeriya

- Tsofaffin Gwamnonin Jihohi na kokarin ganin na su ya samu mukamin

- Daga ciki akwai wani Sanata kuma tsohon Gwamna da ke harin kujerar

Mun samu labari cewa tsofaffin gwamnonin jihohin kasar nan da ke rike da mukaman Sanatoci su na shirin daura wani daga cikin su a matsayin shugaban majalisar dattawa. Wannan zai batawa shirin da jam’iyyar APC ta ke yi.

Wadannan Sanatoci da sun yi gwamna a zamanin da, za su yi bakin kokarin su wajen ganin cewa na su ne ya samu kujerar shugaban majalisar dattawa wannan karo. Tsofaffin gwamnonin jihohin za su hada kai ne a majalisar kasar.

Majiyar tace irin wadannan tsofaffin gwamnoni da ake da su a majalisar dattawa, za su marawa wani daga cikin su baya ne ko da kuwa ba ya cikin jam’iyyar APC mai mulki. Wani Sanata ne dai yanzu haka yake ta wannan shiri.

KU KARANTA: An yi takaddama tsakanin Sanatocin Najeriya a Majalisar Dattawa

Gwamnonin da na neman yi wa Jam’iyyar APC taron dangi a Majalisa ta 9
Sanatoci na yunkurin bijirewa shugabancin Jam’iyyar APC mai mulki a Majalisa
Asali: UGC

Sanatocin da su ka yi gwamna a da, za su goyi bayan wani Takwaran su ne da ya fito daga Arewa maso tsakiya idan an tashi zaben majalisa, ganin yadda ya sa aikin majalisa a gaban sa, a maimakon zama ‘dan amshin shatan APC.

Kamar yadda mu ke samun labari, shirin da ake yi shi ne, wannan Sanata ya hada kai da ‘yan adawa da ke majalisar dattawa wajen ganin ya samu wannan mukami na 3 a Najeriya. Irin haka ne dai Bukola Saraki yayi a 2015.

Tsofaffin gwamnoni da za a samu a majalisa wannan karo sun hada da: Danjuma Goje,Abdullahi Adamu, Orji Kalu, Theodore Orji, Kashim Shettima, Sam Egwu, Gabriel Suswan, Danjuma Goje, Ibikunle Amosun da Chimaroke Nnamani.

Sauran tsofaffin gwamonin a majalisa ta 9 su ne: Ibrahim Shekarau, Tanko Al-Makura, Aliyu Magatakarda Wamakko, Ibrahim Geidam, Abdul’Aziz Yari da kuma Sanata Muhammad Adamu Aliero.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel