Buhari zai inganta gine-ginen manyan tituna da ke Kudu maso Gabas - Onochie

Buhari zai inganta gine-ginen manyan tituna da ke Kudu maso Gabas - Onochie

Lauretta Onochie, hadima ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan dandalan sada zumunta, ta fayyace kudirin Ubangidan ta na habaka ingancin gine-ginen tituna a yankunan Kudu maso Gabas da kuma wasu sassan kasar nan.

Cikin gabatar da jawaban ta a yau Lahadi, Onochie ta zayyana yadda manyan hanyoyin Onitsha zuwa Enugu da kuma Amansea zuwa Enugu suka lashe zunzurutun dukiya da kimanin naira biliyan 5.1 wajen gyara da kuma inganta su.

Wasu ayyukan titi da gwamnatin shugaba Buhari ke aiwatar wa a Kudancin Najeriya
Wasu ayyukan titi da gwamnatin shugaba Buhari ke aiwatar wa a Kudancin Najeriya
Asali: Facebook

Kamar yadda Onochie ta zayyana a shafin ta na zauren sada zumunta, ta ce sabuwar gwamnatin shugaban kasa Buhari a wa'adin sa na biyu ta daura damarar inganta ci gaban gine-ginen tituna a yankunan Kudu maso Gabas da kuma sauran yankunan kasar nan.

KARANTA KUMA: Ba bu batun fitar Jonathan daga jam'iyyar PDP - Hadimin sa

Ta ce dukkanin yankunan kasar nan su zauna cikin shirin c igaba da kwankwadar romo na sabuwar gwamnatin shugaban kasa Buhari kasancewar sa jagora mai matsananci kishin kasa gami da jajircewa da tsayuwa kan gaskiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel