Ba bu batun ficewar Jonathan daga jam'iyyar PDP - Hadimin sa

Ba bu batun ficewar Jonathan daga jam'iyyar PDP - Hadimin sa

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya barrantar da kan sa tare da musanta rahotanni da ke yaduwa da cewar ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne da sanadin mai magana da yawun sa, Ikechukwu Eze, inda ya ce karairayi ne kurum da shaci fadi gami kagaggun zantuttuka da wasu 'yan jarida suka wallafa tare da yadawa al'umma domin cimma wata manufa.

Wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Jonathan ya bayyana rahoton ficewar sa daga jam'iyyar PDP yayin ganawa da manema labarai na kafar watsa labarai ta NNA (Nigeria News Agency).

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista Eze ya ce ba bu ta yadda za a yi tsohon shugaban kasa ya gana da wata kafar watsa labarai da ba ta da wani tushe ko madogara ta asali a kasar nan.

KARANTA KUMA: Ya kamata INEC ta yi watsi da jam'iyyun siyasa 81 na Najeriya - Falana

Ya ci gaba da cewa, ba bu wani dalili a halin yanzu da zai sanya tsohon shugaban kasa ya fice daga jam'iyyar sa ta PDP ba ya ga cewa a karkashin inuwar ta ya rike kujerar mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa da kuma ta shugaban kasa baki daya.

Mista Eze ya shawarci masu sha'awar yada karairayi da zantuka na shaci fadi da su nemi wata hanyar cin abinci ta daban da za ta tabbatar da ingancin rayuwar su da kuma bunkasar ci gaban kasar nan baki daya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel