Ya kamata INEC ta yi watsi da jam'iyyun siyasa 81 na Najeriya - Falana

Ya kamata INEC ta yi watsi da jam'iyyun siyasa 81 na Najeriya - Falana

Fitaccen Lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana (SAN), ya yi tuni ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC kan cewa ta na da ikon watsi da dukkanin jam'iyyu da suka gaza cika wasu sharudda na harkokin siyasa.

A bayanan da ya gabatar a yau Lahadi, Falana ya tabbatar da cika duk wasu sharuddan shiga harkokin siyasa zai zaftare adadin jam'iyyun siyasar kasar nan daga 91 zuwa alal akalli guda goma kacal.

Femi Falana
Femi Falana
Asali: Depositphotos

Sabanin yadda aka saba kuma aka fahimta a baya, hukumar INEC ta na da ikon rage adadin jam'iyyun siyasa. Ya ce hukumar INEC ta samu madogarar wannan iko yayin shimfidar wata sabuwar doka da aka gindaya cikin kudin tsarin mulkin kasa a shekarar 2017 da ta gabata.

Fitaccen Lauya Falana ya hikaito yadda a shekarar 2010 da ta gabata wasu jam'iyyun kasar nan suka cimma nasara wajen kalubalantar shimfidar wannan babban iko da rataya a wuyan hukumar INEC.

KARANTA KUMA: Rashin samun dama da lokacin nutsuwa ya hana mu ba Atiku damar bincikar kayan zabe - INEC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar INEC ta samu alfarmar wannan iko biyo bayan ruwa da tsakin majalisar tarayya da ta shiga kuma ta fita wajen gyara kundin tsarin mulkin kasa domin dawo wa da hukumar INEC martabar ta.

Cikin wani rahoton da shafin jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar rundunar sojin kasa ta Najeriya kamar yadda kakakin ta ya bayyana, Kanal Sagir Musa, ta yiwa wasu manyan dakarun ta sauye-sauyen wuraren aiki a fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel