Binciken daloli: EFCC ta kai same gida da gidan gonar tsohon alkalin alkalai

Binciken daloli: EFCC ta kai same gida da gidan gonar tsohon alkalin alkalai

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kai samame gida da gidan gonar tsohon alkalin alkalan Najeriya da aka dakatar, Walter Onnoghen, tare da yin gaba da wasu muhimman kayayyaki.

A cewar jaridar Punch, kimanin jami’an EFCC 9 ne suka dira gidan gonar Onnoghen dake Masaka a jihar Nasarawa a jiya, Asabar, tare da yin awon gaba da wasu muhimman takardu da su ka hada da takardun shaidar ciniki da rijistar ma’aikata.

An bayyana cewar sun je gidan gonar ne bisa rakiyar jami’an ‘yan sanda kuma shafe fiye da sa’o’i uku suna gudanar da bincike a gidan gonar duk da basu nuna wata shaidar umarnin yin hakan daga kotu ba.

Onnoghen na fuskantar tuhumar kin bayyana ainihin kadarorinsa a gaban kotun da’ar ma’aikata (CCT).

Ya sanar da kotun cewar wasu daga cikin makudan kudin da aka samu a asusun sa ya same su ne ta hanyar noma da canjin kudi.

Wani dan uwa ga Onnoghen ya ce sai da jami’an na EFCC su ka duba har dakunan ajiyar kaya da tankunan adana ruwa suna neman daloli.

Binciken daloli: EFCC ta kai same gida da gidan gonar tsohon alkalin alkalai
Walter Onnoghen
Asali: Depositphotos

Muna gona a jiya, Asabar, da rana sai ga jami’an hukumar EFCC a wata farar mota kirar Nissan da lambar Abuja BWR627AT. Ta karfi suka shigo harabar gidan gonar tare da kayarar duk wanda suka samu a ciki.

“basu gabatar da wata takarda ko nuna shaidar sun samu izini daga wata hukuma ko dalilin zuwansu bag a manajan gidan gonar. Sun birkice ofishinsa tare da yin awon gaba da sunan ma’aikata tun daga watan Fabarairu na sheakarar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Jagoran kamfen din Atiku ya yi murabus daga PDP

“sannan sun tilasta manajan saka hannu a kan takardar cewar basu bincika ko ina ba kuma basu dauki komai ba daga gidan gonar.

“Haka suka yiwa kashiyan gidan gonar; suka kwace takardun shaidar yin ciniki kuma suka tilasta shi saka hannu a kan takarda cewar bai bayar da takardun bisa tilas ko matsin lamba ba,” a cewar dan uwa ga Onnoghen.

Kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade, ya shaidawa manema labarai cewar bashi da masaniyar an kai samame gidan gonar Onnoghen.

A watan Fabrairu ne Onnoghen ya taba aika wasikar korafi zuwa ga rundunar ‘yan sanda a kan cewar wasu makiyaya sun shiga cikin gidan gonar ta sa tare da yin barazana ga ma’aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel