Zaben Ribas: Jam'iyyar APC sun karyata kalaman hukumar INEC

Zaben Ribas: Jam'iyyar APC sun karyata kalaman hukumar INEC

Jama'iyyar adawa a jihar Ribas ta All Progressives Congress (APC) ta karyata kalaman hukumar dake zaman kanta ta kasa dake da alhakin gudanar da zabe ta Independent National Electoral Commission (INEC) akan shigar sojoji cikin harkar zaben gwamnan jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da babban Daraktan jam'iyyar dake kula da harkokin yada labarai na dan takarar gwamnan jihar a APC, Mista Tonye Cole mai suna Tonye Prince will ya fitar.

Zaben Ribas: Jam'iyyar APC sun karyata kalaman hukumar INEC
Zaben Ribas: Jam'iyyar APC sun karyata kalaman hukumar INEC
Asali: Instagram

KU KARANTA: Sojoji sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas

A cewar sa, kamata yayi hukumar zaben ta kasa ta yabawa sojojin da suka taimaka aka gudanar da zaben domin in ba don sun shiga harkokin ba da zaben ma ba zai yiwu ba a mazabu da dama a jihar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa hukumar zaben ta INEC ta fitar da wata sanarwa akan zaben da aka gudanar a jihar ta Ribas inda ta bayyana cewa an yi zabukan a kananan hukumomi 17 cikin 23 kuma jami'an tsaro musamman ma sojoji sun taka rawa wajen tarwatsa tattara sakamakon zabukan.

Haka ma dai hukumar ta INEC a wata sanarwar da ta fitar game da zaben jihar Bauchi, ta bayyana cewa za ta cigaba da tattara sakamakon zaben da a baya ta soko na karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel