"Na tare da Saraki ko daya ba zai shugabanci majalisa ta 9 ba"

"Na tare da Saraki ko daya ba zai shugabanci majalisa ta 9 ba"

Sanata Barista Ovie Omo-Agege dake wakiltar mazabar jihar Delta a majalisar dattawan Najeriya, ya sha alwashin cewa dukkan dan majalisar dattawan dake da wata alaka da Shugaban majalisar na yanzu Dakta Bukola Saraki ta kusa ko ta nesa ba zai shugabanci majalisar ba.

Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayar da haske akan yadda Sanatocin ke shirin zabar shugabannin su a zauren majalisar na gaba da zai shugabance su a wa'adin gaba na shekaru hudu masu zuwa.

"Na tare da Saraki ko daya ba zai shugabanci majalisa ta 9 ba"
"Na tare da Saraki ko daya ba zai shugabanci majalisa ta 9 ba"
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Harin Offa: Barayin sun gogawa Abba Kyari kashin kaji

Legit.ng Hausa ta samu cewa haka zalika Sanatan ya kuma kara da cewa a wannan karon ya zama dole jam'iyyar su ta yi ruwa ta kuma yi tsaki a cikin harkokin zabar shugabannin majalisar domin kaucewa irin matsalolin da suka fuskanta a zauren.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Sanata Ovie Omo-Agege a shekarar da ta shude har dakatar da shi aka yi a majalisar bayan ya tayar da hatsaniya a zauren saboda wasu lamurran da suka shafi jam'iyyar APC da shugaba Buhari.

Shugaban majalisar dattawan dai na yanzu Sanata Bukola Saraki ya rasa kujerar sa ta Sanata wanda hakan ke nufin cewa banda shi za a yi zaman zauren majalisar na 9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel