Jagoran kamfen din Atiku ya yi murabus daga PDP

Jagoran kamfen din Atiku ya yi murabus daga PDP

Gbenga Daniel, darekta janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya sanar da yanke shawarar yin murabus daga zama mamba a jam’iyyar APC da harkokin siyasa.

Jim kadan bayan Daniel ya fitar da wannan sanarwa, gwamnan jihar Ogun da aka zaba, Dapo Abiodun, ya kai ma sa wata ziyara a jiya, Asabar, a gidan sa dake Legas in da suka yi wata ganawar sirri.

A takardar da ya aike ga uwar jam’iyya ta kasa a ranar 14 ga watan Maris, Daniel ya bayyana cewar ya yanke shawarar barin jam’iyyar PDP ne bisa radin kan sa domin ya mayar da hankali a kan wasu harkokin rayuwa.

Kazalika ya bayyana cewar zai yi amfani da lokacin da zai samu domin farfado da kungiyar sa ta jin kai, ‘Gateway Fron Foundation (GFF)’ tare da bayyana cewar zai dawo da aiyukan wata cibiya mai suna ‘non partisan Political Leadership Academy (POLA)’ da aka kafa a wasu shekarun baya domin ilimantar da ‘yan kasa a kan harkokin siyasa.

Jagoran kamfen din Atiku ya yi murabus daga PDP
Atiku da Gbenga
Asali: UGC

A cikin dogon jawabin da ke cikin wasikar ta sa, Daniel ya yi kuka da rikicin da jam’iyyar PDP ta fada a Ogun tun bayan da ta rasa faduwa mulki a jihar a shekarar 2011.

DUBA WANNAN: Sarakuna daga jihohin arewa uku sun ziyarci Buhari, sun nemi ya kirkiri jihar Borgu (Hoto)

Rikicin da PDP ke fama da shi a jihar Ogun ne ya sa Daniel ya fito fili a ranar 9 ga watan Maris kafin a fara zaben gwamna ya nemi magoya bayan jam’iyyar su zabi dan takarar APC, Abiodun.

A zaben gwamnonin da aka kammala, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar da cewar Abiodun na jam’iyyar APC ya samu nasara da kuri’u 241,670 a kan babban abokin hamayyar sa Adekunle Akinlade na jam’iyyar APM wanda ya samu kuri’u 222,153.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel