Kisan New Zealand: Limamin da ke jan sallah, Lateef Alabi ainhin sa ‘Dan Najeriya ne

Kisan New Zealand: Limamin da ke jan sallah, Lateef Alabi ainhin sa ‘Dan Najeriya ne

Jaridar kasar nan ta The Nation ta bayyana cewa daya daga cikin Limaman da ke bada sallolin yini a masallacin Unguwar nan ta Christchurch da ke cikin kasar New Zealand, mutumin Najeriya ne.

Yanzu haka Lateef Alabi shi ne mai tsayawa Ratabin Limamin masallacin unguwar Linwood idan babban Liman ba ya nan. A ranar da wani ‘dan ta’adda ya shiga cikin masallaci ya budawa mamu wuta, Lateef Alabi, ne yake jan sallah.

Allah dai ya tsaga da rabon wannan limami yana da sauran kwana, shiyasa kurum bai mutu ba. Wani Dattijo mai suna A. Abdul Aziz, shi ne yayi na maza bayan da ya karbe bindigar da ke hannun ‘dan ta’addan, ya yi waje da shi.

Wannan Limami, Sheikh Alabi ya bada labarin yadda wannan harin ta’addanci ya auku yayin da yake bada sallah. Alabi yace ya hango wannan mutumi ta tagar masallaci, dauke da bindiga da kimamin karfe 2:00 lokacin ana cikin sallah.

KU KARANTA: Sojoji sun soma binciken yunkurin kisan wani Gwamna a Najeriya

Babban Limamin yake cewa yayi tunanin wannan mutumi wani jami’in tsaro ne, bai fahimci cewa ‘dan ta’adda bane har sai bayan da ya ji an harbe wasu mutum 2 da ke bin sa sallah. Limamin yace ba don an yi dace ba, da an kashe kowa.

Dattijon da ya takawa wannan ‘dan ta’adda mai suna Brenton Tarrant burki, shi ne ya hana a hallaka kowa da ke cikin masallacin inji Limamin na Linwood. Ainihin wannan Mmataimakin Limami dai mutumin Kudancin Najeriya ne.

Har yanzu dai gawar wannan Bayin Allah na nan kwance a cikin masallacin inda jami’an tsaro su ka kewaye wurin ana cigaba da bincike. Limamin dai ya nemi ayi maza a ba su damar yi wa Mamatan jana’iza su bizne su tun da wuri.

Limamin ya kuma nemi ayi maza a sake bude masallacin tare da tabbatar da tsaro a yankin domin a cigaba da yin ibada. Rabon da dai irin wannan mummunan abu ya faru a wannan kasa tun cikin 1983.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel