Masoyin Buhari da ya fara tattaki daga Abuja ya isa Minna, ya nufi Kebbi

Masoyin Buhari da ya fara tattaki daga Abuja ya isa Minna, ya nufi Kebbi

Wani dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Malam Sani Ahmed, da ya fara tattaki daga birnin tarayya Abuja ya isa Minna, babbar birnin jihar Neja domin soyayyarsa ga shugaba Muhammadu Buhari.

Malam Sani ya isa birnin Minna ne misalin karfe 10 na safe bayan ya kwana a Depot na hukumar NNPC.

Ya fara tattakinsa ne a ranar Laraba daga birnin tarayya Abuja kuma zai tafi jihar Kebbi, Zamfara da Sokoto.

Ya kwana a Lambata gabanin shigowarsa Minna inda ya mika sakonsa ga hadimin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello da sabbin sanatocin jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Yaki da hijabi: Kotu ta yankewa wata mata hukuncin bulala 148 da daurin shekaru 38

Yayinda yake magana da manema labaraia Minna, Sani Ahmed yace ya ya fito mika godiyarsa ga gwamnonin jihohin ne bisa ga irin rawar da suka taka a jihohinsu na cigaba.

Yace: "Ina hakan ne domin nuna cewa kungiyar biyayyar APC tana sane da irin ayyukan kwaran da sukeyi da kuma nasarar da suka samu a zaben da aka kammala, muna kara musu karfin gwiwa."

Da aka tambayesa shi yana wannan tattaki ne domin wasu yan kwandaloli, Malan Sani yace shi gamsasshen mutum ne mai sana'ar hannu, saboda haka ba kudi yake nema ba.

A irin wannan lokaci a shekarar 2015, wani masoyin shugaba Buhari, Hashimu Trekker, yayi tattaki daga jihar Legas zuwa Abuja domin yiwa Buhari murnar nasaran zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel