Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin jihar Kaduna

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin jihar Kaduna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da mumunan harin da aka kai a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Buhari ya ce babu wani shugaba da zai kwanta barci hankalinsa kwance alhalin talakawansa na fama da matsalar hare-haren ta’addanci.

An rahoto cewa akalla mutane goma ne aka kashe a wannan hari.

Shugaban kasar yace: “Irin wadannan mutane da ke aikata irin wannan ta’asa ba su da tunanin mutane a zuciyar su.

“Duk da cewa gwamnati tana iya bakin kokarin ganin ta kawo karshen wannan abin tashin hankali dole ne sai suma mutane sun hada kai da gwamnati wajen gani an kawo karshen haka.

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin jihar Kaduna
Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin jihar Kaduna
Asali: Facebook

Buhari ya koka da yadda aka maida komai siyasa a kasarnan har da rayujan mutane ba a dauke shi da daraja ba "Da zarar za ana kokarin bankado irin wadannan mutane masu zuga matasa sai ayi wa gwamnati caaa, cewa wai ba za a tuhumi na su ba.

“Kiyayya da mutane suka saka zukatan su ga juna shine babban dalilin da ya sa ba a iya gano farko ballantana yadda za a iya kawo karshen wannan matsala."

KU KARANTA KUMA: Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna

Baya ga wannan hari da aka kai a Karamar hukumar Sanga, Karamar hukumar Kajuru ma suna fama da irin wadannan hare-hare domin a ‘yan kwanakin nan ma sai da aka rika kai hari kauyukan karamar hukumar Kajuru.

Baya ga irin wadannan hare-hare, kauyuka Birnin Gwari ma na fama da ayyukan mahara da masu garkuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel