Zaben gwamna: Yan asalin jihar Kano mazauna Amurka da Turai sunce suna tare da Ganduje

Zaben gwamna: Yan asalin jihar Kano mazauna Amurka da Turai sunce suna tare da Ganduje

Yan asalin jihar Kano masu aiki a kasashen Turai da Amurka sun aika sakon goyon bayansu ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan zabe zagaye na biyu da za'a gudanar ranar 23 ga watan Maris, 2019.

A wata jawabi da mai magana da yawun Gabduje, Abba Anwar ya saki, ya ce kungiyar masanan sun aiko sakon ne ranar Juma'a, 15 ga watan Maris, 2019.

Game da wasikar, daruruwan yan jihar Kano mazauna Turai da Amurka sun yanke shawara marasa Ganduje baya ta hanyar kira da iyalai da abokansu dake gida da zasu gudanar da zabe zagaye na biyu a jihar.

KU KARANTA: INEC ta hana Atiku duba kayan zabe - Kakakin PDP

Jawabin yace: "Kafin turo wannan wasika mai muhimmanci , a matsayinmu na yan asalin jihar Kani, mun gudanar da bincike kuma mun gamsu da cewa abinda zamu iya yi shine goyon bayan dawowarka,"

"A sani cewa gwamna Ganduje yana kawo cigaba kasarmu. Kuma zamu cigaba da maida hankali kan shugabancin kwarai da gwamnan keyi."

"Tun lokacin da aka sanar da rashin kammaluwan zaben, mun gano cewa Allah ne ya ceci jihar daga shiga wani halin kunci"

"Muna fara tattaunawa daban-daban kan ganin yadda Ganduje zai samu nasara. Muna murnar sanar da cewa gwamnan na kyautata zaton cewa zai yi nasara a zaben."

A bangare guda, Shugaban hukumar bautan kasa NYSC na jihar Kano, Alhaji Ladan Baba yace matasan hukumar tara zasu maimaita shirin bautar kasar na tsawon shekara daya.

Ladan Baba ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai kan yaye matasa masu bautan kasa 2,682 da suka kammala bautarsu a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2019 a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel