Zalunci ba ya dorewa — Kwankwaso

Zalunci ba ya dorewa — Kwankwaso

- Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna rashin gamsuwa da gudanarwar hukumar zabe mai zaman kanta a zaben gwamna da aka dage a jihar Kano

- Kwankwaso ya jadadda cewa zalunci ba abu mai kyau bane

- Babban jigon na PDP a Kano yace kamar akwai banbanci a yadda hukumar INEC ta gudanar da zabe a Kano da irin su Ogun

Babban jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce duk da ba su gamsu da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dauka ba na sake gudanar da zabuka a wasu jihohin kasar, a shirye su ke su shiga domin a fafata da su a zaben da a sake a wasu yankuna na jihar, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Zalunci ba ya dorewa — Kwankwaso
Zalunci ba ya dorewa — Kwankwaso
Asali: UGC

Kwankwaso ya ce, ba wani abu ne ya shi nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris ba, illa su a fahimtarsu kamar akwai zalunci a sakamakon domin suna ganin kamar INEC na da dokoki guda biyu, wato dokar Kano ta 'yan adawa ko kuma wadanda ba a so, da kuma dokar da suka ga ana aiki da ita a wasu jihohi kamar jihar Ogun.

Ya ce dokar da hukumar zabe ta ce idan yawan kuri'un da dan takara na daya samu ba su kai yawan kuri'un da aka soke ba, to sai an sake zabe.

KU KARANTA KUMA: Sojin Najeriya sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas, Wike

Sanatan yace bisa la'akari da yadda suka ga abubuwa na tafiya a wannan zabe da za a sake a wasu wurare a jihar, to za su dauki mataki domin kuwa za su tabbatar da cewa dukkanin akwatunan da za a jefa kuri'a a cikinsu ko da sau 100 za a jefa, to dan takararsu ne zai samu nasara a kansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel