PDP ta kawo kuka: INEC ta hana Atiku duba kayan zabe - Kakakin PDP

PDP ta kawo kuka: INEC ta hana Atiku duba kayan zabe - Kakakin PDP

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi ikirarin cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta ki bin umurnin kotun daukaka kara da ta umurceta da baiwa dan takaran kujeran shugaban kasa, Atiku Abubakar daman duba kayan da akayi amfani da su wajen zabe.

Atiku da jam'iyyarsa sun shiga kotu domin kalubalantar alanta dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), shugaba Muhammadu Buhari, matsayin zakaran zaben 2019.

Jam'iyyar PDP a wata jawabi da ta saki da yammacin Asabar ta bayyana cewa hukumar INEC na kokarin kawowa Atiku cikas wajen kwato hakkinsa da aka kwace masa.

KU KARANTA: Cigaba da sanar da sakamkon zaben Bauchi: Sam ba zamu yarda ba - Jam'iyyar APC

Amma jam'iyyar ta roki INEC da APC su bi umurnin kotu ta hanyar baiwa Atiku daman duba kayayyakin zabe da akayi amfani da su wajen zabe.

Jawabin yace: "Yana da muhimmanci mu sanar da yan Najeriya cewa bayan samun hukuncin kotu, wanda ke baiwa INEC umurnin baiwa Atiku da PDP takardun da akayi amfani da su wajen zaben shugaban kasa."

"Lauyoyinmu sun rubutawa shugaban INEC wasika a ranar 11 da 12 ga watan Maris 2019. Duk da wasikar kotu da wasiku daban-daban da muka turawa INEC, hukumar ta hana PDP da Atiku Abubakar ganin takardu da kayayyakin aikin zabe."

"Shugabancin INEC da APC na kokarin kawo mana cikas a kotu, saboda su gano cewa takardun zaben zai nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben da jama'a suka kada a rumfunan zabensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel