Sojin Najeriya sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas, Wike

Sojin Najeriya sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas, Wike

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai binciki labarin yunkuri kisan Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike da ma zarge-zargen da aka yi wa sojojin na aikata ba dai dai ba lokacin zaben gwamnan jihar.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan na rikon kwarya, Kanal Sagir Musa a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sojin Najeriya sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas, Wike
Sojin Najeriya sun soma binciken yunkurin kisan Gwamnan Ribas, Wike
Asali: Twitter

KU KARANTA: Barayin Offa sun gogawa Abba Kyari kashin kaji

A cewar sanarwar, kwamitin na musamman da aka kaddamar tuni an tura su jihar domin su gano musabbabin yadda lamarin ya auku da kuma shimfida wa sojojin jihar yadda za su cigaba da gudanar da ayyukan su cikin kwarewa da kuma bin doka da oda.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin tarayyar Najeriya, Abdulaziz Yari ya bayyana ikon Allah, kwarewar sa a siyasa da ma kuma irin ayyukan alherin da yayi a jihar sa a matsayin dalilan da suka sa jam'iyyar sa ta APC ta samu nasara a zabukan da aka gudanar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da 'yan jaridar dake a fadar shugaban kasar Najeriya dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, ranar Juma'ar da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel