Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 cif a shafin Instagram

Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 cif a shafin Instagram

- Fitaccen jarumin Kannywood, kuma sarki mai sangaya, Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan daya cif a shafin sadarwa ta Instagram

- Ali Nuhu ne na uku da ya cimma haka bayan Rahama Sadau da Hadiza Gabon

- Ya yi godiya ga mabiyansa akan irin gudunmawar da suka taka wajen taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Babban jarumi kuma darakta a masana’antar shirya fina-finan Hausa Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan daya cif a shafin sadarwa ta Instagram.

Ali Nuhu wanda ya cika shekaru 45 a duniya a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris ya cimma wannan matsayar ne da rukunin abubuwa 6, 303 da ya wallafa a shafin nasa.

Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 cif a shafin Instagram
Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 cif a shafin Instagram
Asali: Facebook

Jarumin kuma manajan darakta a kamfanin FKD Productions, ya zamo mutum na uku da suka cimma hakan baya ga Rahama Sadau da Hadiza Gabon.

Hazalikar jarumin wanda ke bibiyar shafukan mutane 3,062 ya yi bikin murnar wannan wuri da ya kai a rayuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Fadar Shugaban kasa ta yi gum da baki akan tsige mai tsaron Buhari

Ali yayi godiya ga masoyansa da mabiyansa da suke tare da shi tun baya da ya bude shafin nasa na Instagram.

Yace: “Ina godiya ga masoyana da suka kasance tare da ni har zuwa wannan kadamin. Wadanda suka taya ni murnar zagayowar ranar haihuwata da wadanda suka halarci kallon fim din Hafeez da wasan kwallon da kungiyar masoyana suka shirya, Allah ya bar kauna da zumunci.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel