Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna

Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ya jajantawa al'ummar jihar musamman ma iyalan wadanda harin 'yan binda ya shafa a kauyen Nandu dake a cikin karamar hukumar Sanga wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9 da yammacin yau.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin gwamnan na musamman a fannin yada labaru, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ya kuma wallafa a shafukan gwamnan dake dandalin sadarwar zamani.

Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna
Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna
Asali: UGC

UK KARANTA: Yadda APC ta lashe zabe a jihar Zamfara - Gwamna Yari

A cikin sanarwar, Gwamnan ya bayyana kaduwar sa akan harin sannan kuma yayi addu'ar rahamar mahalici ga wadanda suka rasu tare da ta samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka.

Haka zalika Gwamnan ya sake jadda kudurin gwamnatin sa wajen tabbatar da tsaron yan jihar a duk inda suke ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin sarakunan gargajiyar jihar da kuma dukkan jami'an tsaro.

Ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta dauki matakin tura jami'an tsaro a yankin da abun ya auku domin kwantar da hankulan al'umma da kuma hana sake aukuwar hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jihar ta Kaduna na fama da tashe tashen hankula da kashe kashe a wasu sassanta inda akan samu asarar rayuka.

Ga dai takardar manema labaran nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel