Cigaba da sanar da sakamkon zaben Bauchi: Sam ba zamu yarda ba - Jam'iyyar APC

Cigaba da sanar da sakamkon zaben Bauchi: Sam ba zamu yarda ba - Jam'iyyar APC

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) shiyar jihar Bauchi, ta ce sam bata amince da shawaran da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta yanke kan sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa ba.

Jam'iyyar a wata hira da manema labarai ranar Asabar ta ce wannan abu da hukumar INEC ke shirin yi ba zai yiwu ba.

Shugaban jam'iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmed Nana ya ce shawarar da INEC ta yanke ya sabawa kundin tsarin dokar zaben Najeriya.

KU KARANTA: Gwamna El-rufai yayi tsokaci kan kisan mutane 9 a Kaduna

Yace: "Bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya da ka'idojin zaben 2019, hukumar INEC ba tada ikon canza wani janye abinda akayi a cibiyar matattarar zabe inda baturen zabe yayi sanarwa. Kotu kadai take da ikon yanke irin wannan shawara."

Jam'iyyar APC ta tuhumci kwamitin labaran hukumar INEC da kin bata daman fadin ra'ayinta a matsayin jam'iyyar siyasa kafin soke sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

"Hatta mambobin kwamitin abubuwan zargi ne saboda shugaban kwamiti, Festus Okoye, lauya ne kuma abokin kakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara na jam'iyyar PDP."

"Babu wata adalci da wannan shugaban kwamiti zai iya yi saboda yanada nasa ra'ayin kan abubuwan da yake faruwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel