Zaben gwamna: Yadda APC ta lashe zaben Zamfara cikin sa’o’i 24 kacal – Yari

Zaben gwamna: Yadda APC ta lashe zaben Zamfara cikin sa’o’i 24 kacal – Yari

Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya bayyana cewa gamsuwa da yadda yake tafiyar da tsarin shugabanci a jihar Zamfara ne ya mutanen jihar sake zabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar, ga watan Maris.

Gwamna Yari wanda yayi nasarar lashe zaben kujerar dan majalisar dattawa a zaben da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu, ya bayyana haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Zaben gwamna: Yadda APC ta lashe zaben Zamfara cikin sa’o’i 24 kacal – Yari
Zaben gwamna: Yadda APC ta lashe zaben Zamfara cikin sa’o’i 24 kacal – Yari
Asali: UGC

Yace: “Da yawa an yi ta korafi cewa wai na tare a Abuja bana zuwa jiha ta domin duba halin da mutane ke ciki. Abin da basu sani ba shine a kullum ina tare da mutane na a jihar Zamfara kuma babu shakka sun shaida irin romon dimokradiyya da muka rika kwararo musus a duk fadin jihar.

“A dalilin haka ne ya suka saka mana, suka fito suka zabe mu kwansu da kwarkwatarsu.

“Na san yadda jihar Zamfara take, tuna 1999 na ke siyasa a jihar. Na san kowa kuma na san komai. Duka da matsalar da muka samu a tsakanin mu ‘yan siyasa. Na koma kowa na bishi mun sasanta a tsakanin mu. Shine ya sa kuka ga cikin kwanaki biyu kacal jam’iyyar ta yi nasara a zaben gwamna na jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti

“Ba ya ga kokarin taimakawa mutanen jihar da muka yi, shugaba Buhari ya nuna wa mutanen jihar cewa yana tare da su kuma yana iya kokarin sa wajen ganin an kawo karshin ayyukan ‘yan ta’adda da ya gallabi mutanen jihar.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel