Harin Offa: Abba Kyari ya shiga cakwakiya bayan da barayo daya ya goga masa kashin kaji

Harin Offa: Abba Kyari ya shiga cakwakiya bayan da barayo daya ya goga masa kashin kaji

Wasu daga cikin mutanen da aka kama ana tuhumar su da zargin aikata fashin bankunan garin Offa a shekarar da ta gabata sun shaidawa kotun cewa daya daga cikin 'yan sandan dake binciken su, DSP Abba Kyari ya bukaci su gogawa Sanata Bukola Saraki laifi.

Wadanda ake tuhumar da suka hada da Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye da kuma Adeola Abraham sun labartawa kotun haka zalika cewa tursasa su 'yan sandan suka yi da karfin tsiya kan lallai sai sun fada masu wasu bayanai.

Harin Offa: Abba Kyari ya shiga cakwakiya bayan da barayo daya ya goga masa kashin kaji
Harin Offa: Abba Kyari ya shiga cakwakiya bayan da barayo daya ya goga masa kashin kaji
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Danyen mai bala'i ne ga Najeriya ba alheri ba - Sarkin Ife

Daya daga cikin su, Ayoade Akinnibosun ya shaidawa alkalin kotun cewa Abba Kyari ya shaida masa cewa idan har ya fadi sunan shugaban majalisar dattawan, Dakta Bukola Saraki a cikin wadanda suka sa su aikata fashin zai samu lada mai tsoka.

Sai dai shi Ayoade din ya bayyana cewa bai yadda da hakan ba shi yasa ma har yanzu suke cigaba da azabtar da su ba dare ba rana.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin tarayyar Najeriya, Abdulaziz Yari ya bayyana ikon Allah, kwarewar sa a siyasa da ma kuma irin ayyukan alherin da yayi a jihar sa a matsayin dalilan da suka sa jam'iyyar sa ta APC ta samu nasara a zabukan da aka gudanar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da 'yan jaridar dake a fadar shugaban kasar Najeriya dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, ranar Juma'ar da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel