Fadar Shugaban kasa ta yi gum da baki akan tsige mai tsaron Buhari

Fadar Shugaban kasa ta yi gum da baki akan tsige mai tsaron Buhari

Har yanzu fadar Shugaban kasa bata tabbatar da tsige babban mai tsaron Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba awowai da dama bayan wata jaridar yanar gizo ta saki labarin.

Bisa ga rahoton da Premium Times tayi an maye gurbin mai tsaron, Bashir Abubakar, da Idris Kassim Ahmed, daga hedkwatar yan sandan DSS a Abuja.

Da take bayyana abunda taji daga manyan majiyoyi, jaridar tace an umurci Abubakar da yayi gaggawan tafiya wani kwas a wata jami’a a Buenos Aires, Argentina

An tattaro cewa tsige Abubakar ya kasance bisa ga umurni daga Datakta Janar na DSS, Yusuf Bichi.

Fadar Shugaban kasa ta yi gum da baki akan tsige mai tsaron Buhari
Fadar Shugaban kasa ta yi gum da baki akan tsige mai tsaron Buhari
Asali: Facebook

Har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin mai tsaron Buhari a watan Yuli 2015, Abubakar ya kasance mataimakin darakta a hukumar DSS na jihar Bayelsa.

Kakakin Shugaban kasa, Femi Adesina da Garba Shehu basu amsa sakon text da aka tura masu ba akan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Dan uwana ya bani kunya, ya gaza wa mutanen Kwara – Yar’uwar Saraki

A wani lamari na daban, mun ji cewa Uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari a ranar Asabar, 16 ga watan Maris ta ziyarci wadandaginin Ita-Faji ya rufta masu a birnin Lagas a babbar asibitin jihar domin yi masu jaje.

Uwargidar shugan kasar ta mika jajenta ga wadanda lamarin ya cika dasu, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 20, ciki harda yaran makaranta, kamfanin dillancin labaran Naajeriya (NAN) ta ruwaito.

Aisha wacce ta dauki lokaci wajen ziyartan bangaren mata da kananan yara a asibitin, ta yi addu’a kan Allah ya ba iyalan wadanda suka mutu juriya da hakuri.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel