Da duminsa: An kashe mutane tara a sabuwar harin da aka kai a Kaduna

Da duminsa: An kashe mutane tara a sabuwar harin da aka kai a Kaduna

A kalla mutane tara aka kashe tare da kone gidaje 11 a wani hari da mai kama da na ramuwar gayya da aka kai a daren Juma'a a kauyen Nandu na karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna.

A yayin da ya ke tabbatar da harin, Shugaban karamar hukumar Sanga, Mr Charles Danladi ya ce abubuwa sun lafa a kauyen da abin ya faru kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mr Danladi ya ce hukumomin tsaro na karamar hukumar sun dage domin ganin an kwantar da hankulan al'umma domin kare sake afkuwar wani harin na ramuwa.

DUBA WANNAN: Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Da duminsa: An kashe mutane tara a sabuwar harin da aka kai a Kaduna
Da duminsa: An kashe mutane tara a sabuwar harin da aka kai a Kaduna
Asali: Twitter

Ya ce an kira matasan kauyen an kuma basu shawarwari a kan daukan doka a hannunsu da ka iya munana lamarin.

A wata hira da akayi da wani mazaunin kauyen da aka kai harin da ya nemi a boye sunansa, ya ce ana zargin cewa makiyaya ne suka kai harin ramuwar gayya sakamakon harin da aka kai musu kafin zabe inda aka kashe shanu 11 da akuyoyi 28.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel