Zagaye na biyu: Hukumar INEC ta yi alkawarin adalci ga 'yan jihar Filato

Zagaye na biyu: Hukumar INEC ta yi alkawarin adalci ga 'yan jihar Filato

Yayin da lokacin da aka saka domin sake yin zabukan gwamnoni a wasu jahohi ciki hadda jihar Filato ke kara karatowa, hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau INEC ta baiwa dukkan masu masu ruwa da tsaki tabbacin yin adalci ga dukkan bangarorin.

Mallam Halilu Pai, dake zaman kwamishinan hukumar zaben na jihar Filato shine ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar sa da dukkan jam'iyyun siyasar dake jihar da zaben ya shafa a ranar Asabar, garin Jos, babban birnin jihar.

Zagaye na biyu: Hukumar INEC ta yi alkawarin adalci ga 'yan jihar Filato
Zagaye na biyu: Hukumar INEC ta yi alkawarin adalci ga 'yan jihar Filato
Asali: Instagram

KU KARANTA: Wanda ya kashe musulmai a Nuyuzilan ya gurfana gaban kotu

Mai karatu dai zai iya tuna cewa zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Filato ranar Asabar din da ta gabata, 9 ga watan Maris bai kammalu ba sakamakon kuri'un rumfunan da aka soke a jihar sun fi na tazarar dake tsakanin jam'iyyun APC da PDP dake kan gaba.

Haka ma dai sake zaben na zagaye na biyu kamar yadda muka samu ba a jihar Filato ne kadai ba hadda jahohin da suka hada da Kano, Sokoto, Benue da kuma Adamawa dukkan su a yankin Arewacin Najeriya.

Sai dai yayin da jam'iyyar PDP ce ke kan gaba a jahohin Sokoto, Kano, Adamawa da Benue, jam'iyyar APC ce ke kan gaba a jihar Filato din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel