Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti

Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti

Uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari a ranar Asabar, 16 ga watan Maris ta ziyarci wadandaginin Ita-Faji ya rufta masu a birnin Lagas a babbar asibitin jihar domin yi masu jaje.

Uwargidar shugan kasar ta mika jajenta ga wadanda lamarin ya cika dasu, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 20, ciki harda yaran makaranta, kamfanin dillancin labaran Naajeriya (NAN) ta ruwaito.

Aisha wacce ta dauki lokaci wajen ziyartan bangaren mata da kananan yara a asibitin, ta yi addu’a kan Allah ya ba iyalan wadanda suka mutu juriya da hakuri.

Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti
Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta ziyarci wadanda ginin Lagas ya rufto masu a asibiti
Asali: UGC

Ta kuma yiwa wadanda ke kwance a asibiti addu’an samun lafiya. Daya daga cikin wadanda abun ya cika dasu kuma malama a makarantar benen da ya rufto, Easter Samuel ta nuna alhini kan lamarin.

Malamar mai shekara 19, wacce ke samun kulawa a asibitin tayi addu’a ga Allah da kada ta sake fuskantar wannan lamari a rayuwarta.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya

Shugaban likitocin asibitin, Gani Kale, yace yara 10 aka kwantar a asibitin bayan faruwar lamarin.

Aisha ta samu rakiyan tsohon jigon Lagas a mulkin soji, ritaya Birgediya Janar Buba Marwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Pauline Tallen da sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel