Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya

Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya

- Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun harbi tsohon shugaban hukumar NHRC, Farfesa Bem Anweh a kafa

- Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sanda ta jihar Benue (PPRO), DSP Catherine Annene, ta tabbatar da faruwar lamarin

- Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da shi asibitin Gboko, amma daga baya aka mayar da shi asibitin koyarwa na jihar Benue (BSUTH) da ke a Makurdi

Tsohon shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta kasa NHRC, Farfesa Bem Anweh, a ranar Asabar ya tsallake rijiya ta baya baya a yayin da wasu 'yan bindiga suka kai masa hari a kwaryar Gboko, karamar hukumar Gboko da ke jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kaiwa tsohon shugaban hukumar NHRC harin ne da misalin karfe 10 na safiya a wani gidan sayar da man-fetur da ke kusa da Gyado da ke cikin garin Gboko, inda har suka harbe shi a kafa.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sanda ta jihar Benue (PPRO), DSP Catherine Annene, ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta kara da cewa har yanzu rundunar 'yan sanda ba ta samu cikakken bayani kan yadda 'yan bindigar suka kai harin ba.

KARANTA WANNAN: Neman ceto: Buratai da jami'an tsaro na son ganin bayan rayuwata - Timi Frank

Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya
Da duminsa: Tsohon shugaban hukumar NHRC ya tsallake rijiya ta baya-baya
Asali: Depositphotos

Sai dai, mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa ana hasashen 'yan bindigar 'yan bangar siyasa ne, wadanda suka kaiwa tsohon shugaban hukumar ta NHRC hari tare da haddasa rudani a gidan man a yayin da suka ci gaba da harbi a saman iska domin razanar da jama'a.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun bar wajen ba tare da bata lokaci baya bayan kai harin nasu akan Anweh, wanda aka garzaya da shi asibitin Gboko, amma daga baya aka mayar da shi asibitin koyarwa na jihar Benue (BSUTH) da ke a Makurdi.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel