Neman ceto: Buratai da jami'an tsaro na son ganin bayan rayuwata - Timi Frank

Neman ceto: Buratai da jami'an tsaro na son ganin bayan rayuwata - Timi Frank

- Kwamred Timi Frank, ya zargi Laftanal Janar Tukur Buratai da manyan jagororin rundunar soji na shirin kawar da shi daga doron duniya

- Ya bayyana cewa rundunar soji ba ta jin dadin sa kan yadda ya ke tona asirin ganawar sirrin da ake yi tsakanin Buratai, shugaban INEC da Buhari a cikin dare

- Timi Frank ya ce akwai hujjoji karara da suka nuna yadda jami'an soji suka ci karensu ba babbaka a wajen zaben kasar

Tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC na kasa, Kwamred Timi Frank, ya zargi hafsan rundunar sojin sama, Laftanal Janar Tukur Buratai da manyan jagororin rundunar soji na shirin kawar da shi daga doron duniya.

Frank a cikin wata sanarwa a Abuja a yayin da ya ke martani kan wani sakon da rundunar soji ta tsara inda ta kalubalance shi da zama jakadan watsa labaran karya, ya ce babban shirin Buratai da rundunar soji na shirin kashe shi.

Ya bayyana cewa rundunar soji ba ta jin dadin sa kan yadda ya ke tona asirin ganawar sirrin da ake yi tsakanin Buratai, shugaban INEC da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin dare, inda suka kulla makircin da ya baiwa jam'iyyar APC nasara a zaben 2019.

KARANTA WANNAN: PDP a Bauchi ta jinjinawa INEC kan sabon matakinta na zaben Tafawa Balewa

Neman ceto: Buratai da jami'an tsaro na son ganin bayan rayuwata - Timi Frank
Neman ceto: Buratai da jami'an tsaro na son ganin bayan rayuwata - Timi Frank
Asali: Depositphotos

Frank ya ce: "Buratai na bibiyar rayuwata, yana so ya ga bayana saboda ina fadin gaskiya. Ina so 'yan Nigeria da ma al'ummar kasashen waje su sani cewa Buratai da jami'an tsaro ne ke da alhakin duk wani mummunan abu da zai same ni a cikin shekaru masu zuwa tun da dai hafsan sojin ya sha alwashin ganin ya kar ni kasa a duk lokacin da muka yi ido hudu da shi. Amma Allah ba zai barsu ba, na san zai kare ni daga mummunan nufinsu," a cewarsa.

Ya yi nuni da cewa masu sa idon kan zabe da kungiyar hadakar kasashen turai (EU) ta aiko, cibiyar kasashen da ke da 'yanci (IRI), cibiyar demokaradiyya ta kasa-da-kasa (NDI) da kuma sauran masu sa ido a zabe, sun fitar da rahoto kan yadda jami'an rundunar soji suka gallazawa jama'a a yayin gudanar da zaben.

Ya ce: "Baya ga bidiyoyi da tarin muryoyi da hotuna na hujjar da ke nuna yadda jami'an tsaro suka ci karensu ba babbaka a wajen zabe, duk da hakan Buratai da jami'an tsaro na son 'yan Nigeria su yarda da cewa ni jakadan watsa labaran karya ne, kawai saboda ina tona asirinsu akan shirinsu na tafka magudi a fadin kasar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel