PDP a Bauchi ta jinjinawa INEC kan sabon matakinta na zaben Tafawa Balewa

PDP a Bauchi ta jinjinawa INEC kan sabon matakinta na zaben Tafawa Balewa

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta jinjinawa INEC akan hukuncin da ta yanke na ci gaba da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa

- PDP ta ce kwamitin da hukumar zaben ta turo jihar ya gudanar da aikinsa kamar yadda ya dace domin ganin cewa an baiwa jama'a zabin da suka yi

- Jam'iyyar ta ce ba ta da kyakkyawa yakinin akan kwamishinan 'yan sanda da kuma daraktan hukumar tsaro ta SSS

Jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC akan sake nazari tare da sabunta hukuncin da ta yanke na ci gaba da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da aka soke zabenta a makonnin da suka gabata.

Shugaban jam'iyyar, Alhaji Hamza Koshe Akuyam a zantawarsa da manema labarai a Bauchi a ranar Asabar, ya ce kwamitin da hukumar zaben ta turo jihar ya gudanar da aikinsa kamar yadda ya dace domin ganin cewa an baiwa jama'a zabin da suka yi.

"Kwamitin ya yi adalci. Munyi korafi kan zaben jihar, ita kuma INEC ta kafa kwamiti domin bincike, kuma a karshe kwamitin ya yi adalci. A wajenmu, har yanzu muna da kyakkyawan yakini akan INEC. A yanzu dai mun karaya da jami'an rundunar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wadanda suka sauka daga turbasu akan zaben jihar.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa na fice daga jam'iyyar PDP a dai-dai wannan lokaci - Tsohon gwamnan Ogun

PDP a Bauchi ta jinjinawa INEC kan sabon matakinta na zaben Tafawa Balewa
PDP a Bauchi ta jinjinawa INEC kan sabon matakinta na zaben Tafawa Balewa
Asali: Twitter

"Suna sane da dukkanin abubuwan da suka faru na yadda wasu 'yan ta'adda suka je cibiyar tattara sakamkon zabe tare da lalata sanarwar zaben, suna a wajen lokacin da komai ya faru. Amma mun yi mamakin yadda hatta takardar da 'yan sanda ke rike da ita an lalata ta. A lokacin da INEC ta tambaye su, cewa suka yi an lalata su. Shin ba abun mamaki bane ace wani ko wasu suje ofishin rundunar 'yan sanda su lalata takardun zabe?

"Don haka, ba mu da kyakkyawa yakinin akan kwamishinan 'yan sanda, ba mu da tabbas akan daraktan SSS, su ma kusan suna tare ne da M.A Abubakar," a cewar sa.

Idan za a iya tunawa, an ki amincewa da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa bayan da malamar zaben karamar hukumar, Mrs Dominion Anosike ta ce an samu hargisti da kuma rikici a cibiyar zabe.

A cewar ta, wasu 'yan ta'adda sun kai hari cibiyar tattara sakamakon zaben inda suka yaga takardar zaben ta INEC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel