Kotu ta kara kwace wasu biliyoyin naira daga hannun matar Jonathan

Kotu ta kara kwace wasu biliyoyin naira daga hannun matar Jonathan

Kotun koli na tarayya ta jadada hukuncin da babban kotun jihar Legas ta yanke na bayar da umurnin kwace zunzurutun kudi Naira Biliyan 2.4 daga hannun Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Wannan na zuwa ne kwanaki takwas bayan kotun kolin da tabbatar da hukuncin da da babban kotun ta bayar na amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na kwace kudi Dala Miliyan 8.4 da ake kyautata zaton na matar tsohon shugban kasar ne.

Kotun kolin ta kuma umurci Patience ta koma babban kotun na Legas domin tayi bayanin dalilin da ya sa ba ta mika kudin zuwa ga gwamnatin tarayya dundundun ba.

DUBA WANNAN: Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Kotu ta kara kwace wasu biliyoyin naira daga hannun matar Jonathan
Kotu ta kara kwace wasu biliyoyin naira daga hannun matar Jonathan
Asali: Twitter

A hukuncin da alkalai biyar suka yanke a a ranar Juma'a, Kotun koli tayi watsi da daukaka karar da wani kamfanin da EFCC ta gano cewa na Patience Jonathan ne mai suna Lawari Funiture and Bath Limited da aka gano ba shi da nagarta.

Babban lauya Mike Ozekhome ne ya daukaka karar sai dai EFCC ta ce akwai kudade da yawa a kamfanin da ake zargin na haramun ne.

Sai dai a hukuncin da aka karanta a madadin Amiru Sanusi da bai samu halartan kotun ba, kotun koli ta ce ba ta ga dalilin da zai sa ta tayi katsalandan cikin abubuwan da sauran kotunan biyu suka gano ba.

Kotun ta ce idan da akwai wani dalili na karya doka ko karya shine za ta iya canja hukuncin da sauran kotun duka yanke a baya amma tunda ba bu hakan, ba bu wani dalilin da zai sa a soke hukuncin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel