Da duminsa: Ba a samu asarar rai ba sakamakon ruftawar gini a Ibadan - 'Yan sanda

Da duminsa: Ba a samu asarar rai ba sakamakon ruftawar gini a Ibadan - 'Yan sanda

Ma'aiktan ceton gaggawa da ke aikin ceto a wurin ginin da ya rushe a unguwar Bode a jihar Ibadan sun bar wurin bayan kammala nemo wadanda ginin ya rubzowa ba kuma ba bu wanda ya mutu.

A yayin wata hira da ya yi da Tribune Online, Kakakin rundunar 'yan sandan reshen jihar Oyo, Mr Gbenga Fadeyi ya ce an ceto mutane biyar da ginin ya fado a kansu suna samun kulawa a asibiti amma ba bu wanda ya mutu.

"An gama binciken lafiya, babu wanda ya mutu sakamakon rushewar ginin, an ceto mutane biyar kuma tuni an garzaya da su asibiti domin samun kulawa," inji Fadeyi

Da duminsa: Ba a samu asarar rai ba sakamakon ruftawar gini a Ibadan - 'Yan sanda
Da duminsa: Ba a samu asarar rai ba sakamakon ruftawar gini a Ibadan - 'Yan sanda
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

A jiya Legit.ng ta ruwaito muku cewa ginin bene mai hawa biyu ne ya rushe a hanyar Idi-Arere da ke Bode a garin Ibadan inda ya ruftawa mutane 23 amma an ceto shida.

Kangon da ake kan gininsa ya rushe ne misalin karfe 5.30 na yammacin Juma'a a yayin da ake gudanar da aiki kamar yadda wani shedan ganin ido ya ce.

Wani da lamarin ya faru a gabansa, David Aderibigbe da ke zaune kusa da inda ake ginin ya ce a kalla ma'aikata 23 da masu sayar da abinci biyu ne ginin ya rufta musu.

Ya kuma ce mutane shida kadai aka samu damar cetowa.

"Wasu daga cikin wadanda aka ceto daga ginin sun fada mana cewa a kalla akwai ma'aikat 23 da masu sayar da abinci biyu da ginin ya ruftawa.

"Wanda aka ceto ya ce daya daga cikin mai sayar da abincin tana tare da jaririnta," inji Adetibigbe.

A yayin da ya ke tsokaci a kan lamarin, shugaban hukumar taimakon gaggawa na jiha, SEMA, Mr Akin Makinde ya ce lamarin abin tsoro ne inda ya ce hukumar ta sha gagadin masu gini su rika bin ka'idojojin aiki domin kiyaye fitina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel