Wanda ya kashe musulmai a masallacin Nuyuziland ya gurfana a kotu

Wanda ya kashe musulmai a masallacin Nuyuziland ya gurfana a kotu

Babban wanda ake tuhuma da laifin aikata ta'asar ta'addancin kisan musulmai masu sallah har mutum 49 a kasar Nuyuzilan ranar Juma'ar da ta gabata mai suna Brenton Tarrant ya gurfana a gaban wata kotun kasar domin fara shari'ar sa.

Kamar dai yadda muka samu, Brenton Tarrant wanda ke zaman dan asalin kasar Ostireliya mai shekaru 28 a duniya ya bayyana ne a akurkin wadanda ake tuhuma sanye da kayan fursuna kuma hannayen sa daure da ankwa domin soma shari'ar sa.

Wanda ya kashe musulmai a masallacin Nuyuziland ya gurfana a kotu
Wanda ya kashe musulmai a masallacin Nuyuziland ya gurfana a kotu
Asali: UGC

KU KARANTA: Sheikh Gumi yayi magana kan sake zaben Kano

Bayanan da muka fara samu dai sun shaida mana cewa an samu wanda ake tuhumar da bindigogi akalla biyar kuma dukkan su masu rijista. Wannan ne ma ya sa Firaministan kasar ta Nuyuzilan Jacinda Ardern ya ce dole ne su yi gyaran dokar mallakar bindiga.

Sai dai a gurfanarwar ta farko da aka yi wa mai laifin tare da wasu su biyu da ba'a bayyana sunan su ba, ba a karanta masu laifin su ba kuma za su cigaba da zama ne a gidan yari har sai 5 ga watan Afrilu.

Majiyoyin mu dai sun bayyana mana cewa cikin wadanda suka yi shahada a yayin harin sun hada hadda wasu yara masu kananan shekaru da kuma wani dattijo dan kasar Afganistan mai shekaru 71 a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel