'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Otel din wani babban dan siyasa

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Otel din wani babban dan siyasa

Rahoton da muka samu daga Sahara Reporters ya bayyana cewa an harbe wasu 'yan sanda biyu har lahira a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sunyi kai farmaki Odeme Hotel da ke Alamieyeseigha Road a daren Juma'a inda suka kashe 'yan sandan biyu da ke gadi.

Hotel din dai mallakin dai majalisa mai wakiltan mazabar Bayelsa ta tsakiya ne a majalisar wakilai na tarayya, Emmaneul Paulker.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Otel din wani babban dan siyasa
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Otel din wani babban dan siyasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Yan bindigan sun bude wuta ne sannan suka tsere da bindigun 'yan sandan bayan sun kashe su.

Wani shedan ganin ido ya shaidawa majiyar Legit.ng cewar sun dauki kamar mintuna 30 suna musayar wuta kafin suka kashe 'yan sandan.

"Ban san daga inda mutanen suka fito ba amma sunyi mummunar musayar wuta hakan yasa duk mutanen unguwar suka buya. Da muka fito, mun ji wai sun kashe 'yan sanda biyu."

Kawo yanzu, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Bayelsa ba ta riga ta ce komai a kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel