Dalilin da ya sa na fice daga jam'iyyar PDP a dai-dai wannan lokaci - Tsohon gwamnan Ogun

Dalilin da ya sa na fice daga jam'iyyar PDP a dai-dai wannan lokaci - Tsohon gwamnan Ogun

Rahotanni da ke cimmana a dai-dai wannan lokaci na nuni da cewa, Mr Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun kuma babban mai tsara yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi murabus daga harkokin siyasa gaba daya.

Mr Daniel, wanda ya kasance babban jigo a jam'iyyar PDP na tsawon lokaci, a cikin wasikarsa da ya aikewa shugaban jam'iyyar, Uche Secondus, ya ce ya yi murabus daga siyasa biyo bayan gane cewa ya kai koluluwar muradinsa a siyasar.

A yanzu dai Mr Daniel zai ci gaba da gudanar da rayuwarsa bayan murabus, yana mai ci gaba da kula da gidauniyarsa ta tallafi, kamar yadda ya ce a cikin wasikar tasa da ya rubuta a ranar 14 ga watan Maris.

KARANTA WANNAN: INEC ta sauya ra'ayi kan zaben Bauchi, za ta sanar da sakamakon Tafawa Balewa

Dalilin da ya sa na fice daga jam'iyyar PDP a dai-dai wannan lokaci - Tsohon gwamnan Ogun
Dalilin da ya sa na fice daga jam'iyyar PDP a dai-dai wannan lokaci - Tsohon gwamnan Ogun
Asali: UGC

A watan Mayu 2018, Atiku Abubakar ya tabbatar da nadin Mr Daniel a matsayin daraktan yakin zabensa. Amma bayan samun nasarar Mr Abubakar a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP da ya gudana a watan Oktobar 2018, sai aka sauke Mr Daniel daga mukamin daraktan yakin zaben, aka maye gurbinsa da Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai.

Majiyoyi da dama sun shaidawa jaridar PPREMIUM TIMES ta ranar Asabar cewar murabus din Mr Daniel ya biyo bayan yadda ta kaya a zaben shugaban kasa, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lallasa Mr Atiku da kusan tazarar kuri'u miliyan hudu.

Sai Mr Daniel ya ke ganin kamar cewa ya gaza gudanar da aikinsa yadda ya kamatawa jam'iyyarsa, kuma har ya zama silar ciresa daga shugabantar kwamitin yakin zaben, a cewar wata majiya dake kusa da tsohon gwamnan.

Sai dai har yanzu Mr Daniel bai fito bainar jama'a ya sanar kalubalanci matakin Atiku na tsige shi tare da maye gurbinsa da Mr Saraki ba, amma dai a cikin wasikar ta sa ya jaddada cewa ya yi murabus daga siyasa ne a kashin kansa ba wai wata takura ta jam'iyya ba.

Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar PDP, ya shaidawa PREMIUM TIMES ta ranar Asabar cewa bai ga wasikar da Mr Daniel ya aikewa jam'iyyar ba, don haka ba zai iya cewa komai akan maganar ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel