Zaben 2019: Gwamnan Zamfara ya bada labarin yadda jam'iyyar APC ta samu nasara a jihar sa

Zaben 2019: Gwamnan Zamfara ya bada labarin yadda jam'iyyar APC ta samu nasara a jihar sa

Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin tarayyar Najeriya, Abdulaziz Yari ya bayyana ikon Allah, kwarewar sa a siyasa da ma kuma irin ayyukan alherin da yayi a jihar sa a matsayin dalilan da suka sa jam'iyyar sa ta APC ta samu nasara a zabukan da aka gudanar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da 'yan jaridar dake a fadar shugaban kasar Najeriya dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, ranar Juma'ar da ta gabata.

Zaben 2019: Gwamnan Zamfara ya bada labarin yadda jam'iyyar APC ta samu nasara a jihar sa
Zaben 2019: Gwamnan Zamfara ya bada labarin yadda jam'iyyar APC ta samu nasara a jihar sa
Asali: UGC

KU KARANTA: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a Kano

Gwamnan a cikin bayanan sa ya bayyana kwarewar sa a siyasa da ya samu dalilin zaman sa shugaban jam'iyyar ANPP na wancan lokacin da kuma dan majalisar tarayya na shekara hudu da kuma Gwamna na shekara takwas a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka taimaka masa a zaben.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jam'iyyar APC ta jihar Zamfara ta shiga rudani sosai tun bayan zabukan fitar da gwamnin takarar gwamna da aka gudanar a watan Satumba da ya gabata inda har hukumar INEC da farko taki amincewa da shigar jam'iyyar takara a zaben.

Sai dai kuma kimanin sauran Sati daya wata kotun daukaka kara dake a Jihar Sokoto ta yanke hukuncin barin jam'iyyar tayi takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel